Featured
Tinubu ya yaba da hukuncin koton koli kan ‘yancin kananan hukumomi

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da hukuncin kotun koli da ya tabbatar da ‘yancin kananan hukumomi.
Chief Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis ya ce, Tinubu yayi bayanin cewa babban kalubalen dake shafar ci gaban kasarnan tsawon shekaru nada alaka da rashin gudanar da mulkin kananan hukumomi yadda yakamata.
Acewar shugaban kasar, kamar ba a tafikar da gwamnati a matakan kananan hukumomi wadanda sune na kasa-kasa.
Tinubu yayi bayanin cewa yanzu lokaci ne da ya ragewa shugabannin kananan hukumomi wajen yin ayyukan da zasu shafi al’umma.
Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta shigar da karar ne bisa aminta da tayi cewa dole ne ‘yan Najeriya su samu sauki.