Featured
Tsadar Rayuwa: Ya Kamata Malamai Su Gana Da Shugaban Kasa Don Sanar Da Shi Halin Da Al’umma Ke Ciki – Daurawa

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya yi kira ga Malamai da su nemi ganawa da shugaban kasa domin sanar da shi halin da ake ciki na tsadar kayayyakin masarufi kamar yadda suka yi a lokacin rikicin kasar Nijar.
Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook da X a ranar Lahadi.
“Muna roko ga malamai su shiga tsakani kamar yadda suka shiga a Nijar,
lallai su nemi ganin shugaban ƙasa, da shugabanan majalisar dattijai, da na wakilai, da shugaban majalisar gwabnoni,
da duk masu faɗa a ji, a gaya musu gaskiya domin kawo ƙarshen wannan tirka-tirka.
” A ci gaba da haƙuri da aiki”, inji Malamin.
Bayanan Daurawa dai na zuwa ne a daidai lokacin da matasa ke shirin fita zanga-zanga don bayyana damuwarsu kan tashin gwauron zabi da kayayyaki suka yi.
A gefe guda kuma ana samun sabanin kan halaccin fita zanga zangar tsakanin bangarorin Malamai.