Featured
Ashura: ‘Yan Sanda Sun Hana ‘Yan Shi’a Gudanar Da Muzahara A Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta dakatar da duk wani gangami da ya saba doka da kungiyar ‘yan uwa Musulmai ta IMN za ta yi ciki har da na Muzaharar ranar Ashura.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Mansir Hassan ne ya sanar da hana gangamin a sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi a Kaduna.
Hassan ya ce “Yan sanda sun dakatar da duk wani nau’in zanga-zanga a jihar.
” Hakan ya faru ne bayan samun bayanan sirri kan cewa mabiya Shi’a na shirin gudanar da tattakin ranar Ashura”.
Acewar ‘yan sandan mabiya kungiyar na amfani da tattakin ne wajen haifar da tarzoma da tada zaune tsaye.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Dabgi yayi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu bisa bin doka ba tare da tsoro ba.