Featured
Bunkasa fannin masana’antu a Najeriya ne yasa ban mallaki gida a kasar waje ba

Wanda yafi kowa kudi a Afrika, Alhaji Aliko Dangote yayi bayanin cewa burin da yake da shi bunkasa fannin masana’antu a Najeriya ne yasa bai mallaki gida a wajen kasar ba.
Yayin ganawa da manema labarai a matatar mai mallakinsa dake Ibeju-Lekki a jihar Legas, Dangote ya ce sau 1 ya taba mallakar gida a London wanda kuma ya siyar da shi a shekarar 1996.
Ya kara da cewa “Dalilin da yasa bani da gida a London ko America shi ne ina son na mayar da hankali wajen bunkasa fannin masana’antu a Najeriya.
” Na gano cewa idan ina da gidaje a can hakan zai nasa na dinga yawan ziyara wanda hakan kuma zai raban hankali.
“Ina da buri sosai wajen cikar muradin Najeriya kuma baya ga gidana na Legas gida 1 ne dani a Kano da kuma wanda nake haya a Abuja”.