Featured
Kotu ta sanya ranar sauraron daukaka kara kan rikicin masarautar Kano

Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta sanya ranar 12 ga watan Agusta don sauraron karar da aka daukaka kan rikicin masarautar Kano.
Mai shari’a Hamma Akawu-Barka wanda ya jagoranci alkalan kotun 3 ne ya sanya ranar bayan lauyan wanda ya daukaka kara, Chikamso Ojukwu a bukatar da ya gabatar da baki ya nemi a cire mutum guda daga wadanda ake kara.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Mahmoud Mogaji ya soki rokon inda kotun ta bada umarnin a mika bukatar a rubuce.
Gwamnatin Kano da Antoni janar da majalisar dokoki ne dai suka shigar da daukaka karar, haka kuma tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero shima ya daukaka kara.
Masu daukaka karar suna suka kan umarnin da mai shari’a, Abdullahi Liman ya bayar na soke aiwatar da dokar masarautu ta 2024.
Sai Aminu Ado Bayero dake son kotun daukaka karar ta soke umarnin babbar kotun jihar Kano na hana ayyana kansa a matsayin Sarki inda ya ce an yanke hukuncin cikin hanzari a ranar 15 ga watan Yuli maimakon 18 ga watan da aka tsara.