Featured
Gwamnan Katsina ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa yayin da ya tafi hutun wata 1

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya mika ragamar mulkin jihar a hannun mataimakinsa a yayin da ya tafi hutu na wata daya.
A wata wasika da Gwamnan ya aikawa shugaban majalisar dokoki na jihar Katsina, Hon. Nasir Yahya Daura, ya ce hutun zai fara ne daga ranar Alhamis 18 ga watan Yuli na 2024.
Wasikar ta ce a yayin da gwamnan ke tafiya hutu, mataimakinsa, Faruq Lawal Jobe, ne zai ci gaba da jan ragamar mulkin jihar.