Featured
Majalisar Dattawa ta cire Ndume daga mukaminsa

Majalisar dattawa a yau Laraba ta sanar da cire Sanata Mohammed Ali Ndume daga mukamin babban mai tsawatarwa na majalisar.
Yayin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya nemi jin ra’ayin yan majalisar na jam’iyyar APC sun goyi bayan cire Ndume daga mukamim.
An maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa.
Hakan na zuwa ne bayan Sanatan ya soki gwamnatin shugaban kasa Tinubu a yayin da al’umma ke cikin matsin tattalin arziki.
A wata wasika da shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya aikawa ‘yan majalisar APC ya nemi Ndume ya yi murabus daga jam’iyyar.
Wasikar dai na dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje da Sakatarenta, Barista Ajibola Bashiru.