Featured
Mataimakin Gwamnan jihar Edo ya fice daga PDP zuwa APC

Mataimakin Gwamnan jihar Edo wanda kotu ta dawo da shi bayan an tsige shi, Comrade Philip Shaaibu ya jagoranci tawagar magoya bayan jam’iyyar PDP zuwa APC a jihar.
A ranar 21 ga watan Satumba ne dai za a gudanar da zaben Gwamnan jihar ta Edo.
Wadanda suka bar jam’iyyar ta PDP sun hada da Charles Idahosa mamba na kwamitin amintattu na PDP da tsohon shugaban majalisar dokokin jihar, Hon. Kabir Adjoto da sauran manyan jiga jigan jam’iyyar ta PDP.
Da yake jawabi yayin bikin, Shaibu ya ce sun shiga jam’iyyar ne domin dawo da jihar Edo ga mutanen jihar.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Adams Oshiomhole ne suka karbi tawagar ta PDP zuwa APC.