Featured
‘Yan Najeriya sun bukaci a kori shugaban hukumar NMDPRA bisa kalamansa kan matatar mai ta Dangote

Ƴan Najeriya sun yi kira da a kori shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa, Farouk Ahmed bisa kalaman da yayi na cewa man dizel din da matatar mai ta Dangote ke samarwa bai kai kyan wanda ake shigo da shi Kasar nan ba.
‘Yan Najeriyan na ganin kalaman nasa kamar kashe gwiwa ne da shafawa matatar man ta Dangote bakin fenti.
Tun da farko dai Ahmed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta hana shigo da albarkatun man fetur Kasar nan ba, inda ya ce kasar ba za ta dogara da matatar mai daya ba.
Da yake mayar da martani kan zargin cewa hukumar NMDPRA ta bai wa wasu yan kasuwa lasisin shigo da gurbataccen mai Najeriya, Ahmed ya ce man na Dangote ne ke dauke da gurbatacce nau’i.
Sannan ya ce matatar wacce ke siyar da man dizel da na jirgin sama ba ta da cikakken lasisi har yanzu.
Sai dai wasu ‘yan Najeriya a shafin X sun bukaci a sauke shugaban hukumar saboda kalaman nasa inda wani mai suna Ohiozoje Augustine ya ce “Ya kamata a sauke shi nan take domin kalaman nasa ka iya haifar da illa”.
Inda karin mutane da dama ke ganin kalaman a matsayin na kashe gwiwa ga matatar man mafi girma a Afrika.