Featured
Ambaliya ta tilastawa Shehun Borno barin fadarsa

A safiyar Talatar nan ne Ambaliyar ruwa ta cinye fadar Shehun Borno, Alhaji Garba Elkenemi, da wasu sassa na garin Maiduguri babban birnin jihar.
Jaridar Punch ta rawaito daga mazauna yankin cewa, tuni Shehun Borno ya fice daga fadar inda a halin yanzu yake zaune a gidan gwamnatin jihar.
Wani mazaunin Kofar Shehu yace,” Wannan abin tsoro ne, ban taba ganin irin haka a Maiduguri ba tun da nake, hatta Shehun Borno yanzu ya fita daga fadar sa saboda ambaliyar “.
Wakilin KAKAKI24 dake Maiduguri ya tabbatar da cewa wuraren da Ambaliyar tafi ƙamari sune Lagos Street da Maiduguri da Post Office da kuma Gwange. Ya kara da cewa, ” An fada mana ga Ambaliya nan, amma bamu yi tsammanin ganin haka ba.