Connect with us

Featured

Dubun Matasan da suka yi garkuwa da Yaro ɗan shekara hudu ta cika

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu mutane uku, da ake zargi da yin garkuwa da wani karamin yaro ɗan shekaru hudu a duniya, wadanda suka Nemi kudin fansar naira Miliyan 10.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labari a jiya Litinin 09 ga Satumba, 2024.

Kiyawa yace, anyi garkuwa da yaron mai suna Muhammed Nasir Jamilu, mazaunin Sharada a Kano, a ranar 7 ga watan Satumba 2024, Inda waɗanda ake zargi suka kai shi maɓoyarsu dake karamar hukumar Gwarzo, daga bisani suka karbi naira dubu dari uku 300,000, kafin a cika mu su ragowar kudin.

Wadanda ake zargin sun hada da Hisbullah Salisu, mai Shekaru 30, da Hassan Ali Rabi’u, mai Shekaru 28, dukkaninsu mazaunan unguwar Yakasai, sai kuma Hassan Ali mai Shekaru 22, mazaunin unguwar Hotoro.

Bayan ceto yaron an kai shi Asibitin Murtala Muhammed, dake Kano domin duba lafiyarsa, kuma a halin yanzu tuni an mika shi hannun iyayensa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet