Featured
Tinubu Ya San Cewa Matakan Da Yake Dauka Suna Da Tsauri – Gwamna Sule

Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, yace Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana da masaniyar cewa matakan da yake dauka suna kara jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Gwamnan Sule, ya bayyana haka ne a jiya Talata 29, ga Oktoba 2024, a cikin wani shiri na gidan talabijin na Channels, yace dama babu inda Shugaba Tinubu yace matakan da zai dauka za su zo da sauki, amma ya tabbatar da cewa nan gaba kadan kowa zai ji dadi a Najeriya.
Jaridar KAKAKI24, ta rawaito cewa, tun bayan da Shugaba Tinubu ya karbi mulki a Hannun tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a shekarar 2023, Yan Najeriya suka shiga wani hali sakamakon tsauraran matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka, kamar su cire tallafin man fetur da sauran su.
A cewar Sule, “Tabbas Shugaba Tinubu yasan halin da ake ciki a kasar nan, kuma ya damu, dama tun farko babu Wanda yace matakan za su zo da sauki dole matakai ne masu tsauri, kuma wannan yanayi na matsi dole ne sai an fuskance shi, amma na dan lokaci ne komai zai dawo dai dai”.