Featured
Suman ƙarya yara suka yi a kotu- IGP

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayyana cewa, Yaran da suka suma a kotu su shida cikin waɗanda aka gurfanar bisa zargin cin amanar kasa yayin zanga-zangar tsadar rayuwa sun yi hakan ne da gangan domin ɗaukar hankali da ɓata sunan hukumomi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan Muyiwa Adejobi ya fitar a madadin Sufet Janar ɗin, kakakin ya jadda cewa a ƙarƙashin dokokin Najeriya duk mutumin da ya kai shekarun munzalin aikta laifi, to alhakin wannan laifi da ya yi ya rataya a wuyansa ko yaya shekarunsa suke.
Sanarwar ta ce laifukan da ake tuhumar mutanen da aikatawa sun haɗa da lalata kayan gwamnati da barazana ga tsaron ƙasa da sauransu.
Alƙalin kotun ya bayar da belin kowannensu a kan naira miliyan goma da kuma mutum biyu masu tsaya wa kowanne.
An dai gabatar da masu zanga-zangar ne su 114 ranar Juma’a a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda kafin gurfanar da su, huɗu daga cikin su da suka hadar da yara biyu suka faɗi, inda aka garzaya da su zuwa asibiti.