Featured
Gwamnatin Kano Ta Buƙaci Waɗanda Ba Su Sabunta Takardun Mallakar Ƙasa Ba, Su Gaggauta Yi Kafin 31 Ga Janairun 2025

Ma’aikatar kasa da tsare tsare ta Jihar Kano, ta bukaci Al’ummar Jihar, wadanda basu sabunta takardun mallakar kasa ba, da su gaggauta zuwa hukumar domin sabuntawa, kafin ranar 31 ga watan junairun shekara mai kamawa ta 2025.
Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Kwamishinan kasa da tsare tsare na Jihar, Hon. Abduljabbar Muhammad Umar, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro manema labarai da ya gudana a safiyar yau laraba a Jihar.
Kwamishinan yace, tun a ranar 25 ga watan Nuwambar da ya gabata, Gwamnan Kano Abba Kabir-Yusuf, ya sanar da fara tantance takardun mallakar kasa, yayin kaddamar da hukumar tattara bayanai akan kasa. don haka ne hukumar ta ke kira ga jama’a, da su gaggauta sabunta takardun nasu, kafin 31 ga watan junairun 2025, don kare kadarorin su.
Abduljabbar Umar ya kara da cewa, wannan sabon tsari da Gwamnati tayi, yana da Alfanu da dama, wadanda suka hada da samun sahihan bayanai na mallakar fili, wanda akayi amfani da na’urar zamani, kazalika Takaradar na dauke da tanadi na tsaro, dan kareta daga batagari masuyin takardun bogi.