Featured
Hukumar DSS Ta Biya Wani Mutum Diyyar Miliyan 10 Sakamakon Harbin Kuskure

Hukumar tsaron ta fari kaya a Kasa DSS ta biya wani mutum a Sokoto diyyar naira miliyan 10 saboda harbinsa da ta yi cikin kuskure, bayan an kwashe shekaru 6 ana takun saka.
Shugaban Hukumar Adeola Ajayi ya biya diyyar naira miliyan 10 tare da kuma ƙara masa wasu naira miliyan 10 saboda irin halin ƙuncin da ya samu ƙansa tun lokacin da aka samu kuskure, abinda ya kai ga sashi rasa sana’arsa da kuma rasuwar ƴaƴansa guda biyu.
Su dai jami’an hukumar a ranar 2 ga watan Afrilun shekarar 2016 suka kutsa gidan mutumin a garin Jos, inda suka ɗirka masa bindiga a cinyarsa, akan tunanin cewar wani mutum da suke nema ne wanda ke safarar makamai.
Daga bisani suka dauke shi zuwa babban asibitin koyarwar JUTH inda suka aje shi, suka kuma yi tafiyarsu, bayan sun kama assalin mutumin da suke nema, wanda sunan sa ya yi kama da wanda suka harba.
A cikin yanayin jinyar da ta kassara harkokin kasuwancin sa, mutumin ya rasa yaransa guda 2 da suka mutu, bayan ya koma Sokoto domin ci gaba da kula da kansa.
A ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 2018, kotu a Bauchi ta yanke hukuncin a biya shi diyyar naira miliyan 10, amma Hukumar DSS a ƙarkashin Lawal Daura ta ɗaukaka kara akan hukuncin.
A shekarar 2019 kotun ɗaukaka kara a Jos ta tabbatar da hukuncin ƙaramar kotun, amma sai Hukumar DSS taki aiwatar da shi wajen biyansa kuɗin.
Wannan ya sa mutumin ya rubuta wasikar roƙo ga DSS ta hannu ofishin ministan shari’a, kuma aka dace sabon shugaban hukumar Ajayi ya amince a biya shi diyyar, yayin da ya kuma ƙara masa ƙyautar naira miliyan 10 akai.
Mutumin da aka bai wa kuɗin ya ce yayi asarar jarinsa na cinikin takin zamani na naira miliyan 5 wajen jinya da kuma kula da iyali, tare da cin bashin wasu naira kusan miliyan 9.
Rahotanni sun kuma ce Ajayi ya bukaci likitocin DSS da su duba lafiyar mutumin da kuma taimaka masa ganin irin halin da ya samu kansa na yadda da kyar yake iya tafiya yanzu.