Connect with us

Featured

Rivers: Shugaba Tinubu Ya Sanya Dokar Ta-ɓaci Tare Da Sauke Gwamna Fubara

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas biyo bayan dambarwar siyasar da ake ciki a jihar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasar a talabijin a ranar Talatar nan, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa Ngozi Odu da da dukkan ‘yan majalisar na tsawon watanni shida.

Shugaban kasar ya nada Vice Admiral Ibokette Ibas mai ritaya a matsayin mai kula da harkokin soji da zai jagoranci al’amuran jihar na tsawon watanni shida na farko.

“Ya ku ‘yan Nijeriya, na damu ƙwarai da gaske a kan yanayin da muka samu kanmu da rikicin siyasa a Jihar Rivers. Kamar da yawanku, na bibiyi abubuwan da ke faruwa da fatan ɓangarorin biyu da abin ya shafa za su hankalta a samu mafita cikin ƙanƙanin lokaci, amma dukkan wani fata ya gushe na samar da mafita ga dambarwar,” a cewar Shugaban Kasar cikin jawabinsa.

Shugaba Tinubu ya dogara ne da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin 1999 wajen ayyana dokar. Sashen ya fassara dokar ta-baci a matsayin yanayi na hatsari ko bala’i na kasa inda gwamnati ta dakatar da tsarin mulki na yau da kullum don sake samun iko.

Dokar ta-baci ta bai wa Shugaban Kasa damar yin duk wasu ka’idoji da ake bukata don tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kimanin watanni biyu kenan, da aka kasa kawo karshen cece-kuce da takun sakar mulki tsakanin ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike; da kuma tsohon yaronsa na siyasa, Gwamna Siminalayi Fubara kan kula da tsarin siyasar jihar mai arzikin man fetur.

Rahotanni sun ce bututun mai sun fashe a jihar yayin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda ma’aikatan gwamnati suka yi barazanar gudanar da zanga-zangar adawa da kungiyar Martins Amaewhule a majalisar dokokin kasar masu biyayya ga Wike.

Tinubu ya ce, “Rahotanni na tsaro na baya bayan nan da aka samu sun nuna cewa tsakanin jiya zuwa yau an samu tashin hankali na fasa bututun mai da wasu ‘yan bindiga suka yi ba tare da gwamnan ya dauki wani mataki na dakile su ba, ba shakka na ba jami’an tsaro tsauraran matakan tabbatar da tsaron rayukan al’ummar Jihar Ribas da bututun mai.

“Da wadannan da ma wasu da dama, babu wani Shugaban Ƙasa nagari mai kishin kasa da zai tsaya sakaka ya bar halin da ake ciki ya ci gaba ba tare da daukar matakan gyara da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada ba don magance al’amuran da ke faruwa a jihar, wanda ko shakka babu na bukatar daukar matakai na musamman don dawo da kyakkyawan shugabanci, zaman lafiya, oda da tsaro,” Tinubu ya ce.

A makon da ya gabata ma Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin bin doka da oda a Jihar Rivers domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da ci gaba, a yayin da yake jawabi ga shugabannin siyasa na yankin Kudu-maso-Kudu a Abuja.

Ya shawarci shugabannin da su kasance masu zurfin tunani da rashin son-kai da kuma mai da hankali kan hangen nesa na ceto yankin, a siyasance da tattalin arziki, ta hanyar dagewa wajen mutunta dokokin shari’a na kundin tsarin mulkin kasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet