Featured
Wasu ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC Mai Mulki

Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka daga babbar jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC.
Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ne ya sanar da sauya shekar a cikin wata wasika da aka karanta a zauren majalisar a ranar Talatar nan.
‘Yan majalisar dai Adamu Tanko mai wakiltar Suleja, Gurara, da Tafa na jihar Neja, da Jallo Husseini Mohammed, mai wakiltar mazabar Igabi ta Kaduna, sun bayyana sauya shekar tasu ne a wata wasika da kakakin majalisar Dokta Tajudeen Abbas ya karanta a zauren majalisar.
Da suke bayyana rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP a matsayin dalilinsu na sauya sheka jam’iyyar, masu sauya shekar sun kuma bayyana cewa akidunsu na siyasa a yanzu sun fi dacewa da na APC.