Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Hayar Sojoji Daga Ƙetere Domin Horas Da Dakarunta

Gwamnatin tarayya kasar nan za ta ɗauko hayar ƙwararrun zaratan sojoji daga ƙasashen duniya domin horar da sojojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ƴan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su.
Babban Ministan Tsaron Kasar nan Alhaji Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu.
Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su ci gajiyar wannan horaswar, yayin da daga bisani wasu 800 kuma su biyo baya.
Badaru ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin tinkarar matsalar ƴan ta’adda waɗanda su ma ke sauya dabaru a kodayaushe.
Kodayake ministan bai sanar da sunayen ƙasashen da za a ɗauka hayar waɗannan zaratan sojojin ba, amma ya ce za a ɗauko su ne daga wasu ƙasashen duniya bakwai.
A zangon farko kaɗai, jumullar sojojin Najeriya dubu 2 da 400 ne za a fara bai wa horan na musamman a zangon farko, kafin a tsallaka zuwa zango na biyu.
Ministan ya bayyana cewa, ana samun kwanciyar hankali a wasu yankunan ƙasar sakamakon yadda gwamnati ta dukufa wajen magance matsalar tsaro, inda har ya bada misali da yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, yankin da a cewarsa, an samu zaman lafiya a yanzu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar ƴanbindiga musamman a yankin arewacin Najeriya, inda suke garkuwa da jama’a domin karɓar kuɗin fansa, yayin da a wasu lokuta suke aiwatar da kisa.