Addini
Sarkin Kano Ya Bukaci A Dauki Kwakkwaran Mataki Kan Kisan ‘Yan Kano A Jihar Edo

Mai martaba sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammad Sunusi na II ya yi kira da a dauki kwakwarren mataki kan batun kisan ‘yan jihar Kano a Edo.
Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da hudubar sallar idi a masallacin idi na cikin birni da ke Kofar Mata a ranar Lahadin nan.
“Yadda wasu daga cikin mahukunta suka magantu kan batun kisan abin a yaba ne, amma akwai bukatar duk mai ruwa da tsaki ya tabbatar da an dauki hukuncin ladabtarwa kan duk mai a hannu cikin aika-aikar” in ji shi.
Sarkin na Kano ya kara da jan hankalin matasa musamman a nan Kano akan su gujewa daukar fansa kan abokan zamansu, yana mai cewa ramuwar gayya haramun ce a addini.
Baban Limamin Kano Farfesa Sani Zaharadden ne ya jagoranci sallar idi wadda da ta samu halartar hikimai da kwamishinonin gwamnatin Kano da kuma daruruwan jama’a.