Featured
Gwamnonin PDP 11 Sun Garzaya Kotun Koli Don Jin Ko Shugaban Kasa Na Da Ikon Sanya Dokar Ta-Baci a Jihar Rivers ?.

Gwamnonin jam’iyyar adawa a Najeriya(PDP) guda 11, sun garzaya kotun kolin kasar nan suna kalubalantar ikon da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke da shi na dakatar da tsarin dimokuradiyya a wata jiha.
Ƙarar da gwamnonin suka shigar a ranar Talata 08 ga Afrilu 2025, tana kuma kalubalantar ayyana dokar ta-baci da shugaban kasa yayi a Jihar Rivers.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Kotun Koli, Dr. Festus Akande, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar The Punch.
A ranar 18 ga watan Maris, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyar Gwamna, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Bayan wannan mataki, Shugaba Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin mai gudanarwa na musamman domin jagorantar harkokin jihar.
Kuma tuni majalisar dokokin kasar nan ta goyi bayan matakin da Shugaban Ƙasa ya ɗauka na dakatar da gwamnatin jihar.
Sai dai a wani yanayi na fusata, Gwamnonin PDP guda 11 sun garzaya Kotun Koli don kalubalantar dakatarwar, ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, da kuma naɗa mai gudanarwa na musamman.
Ƙarar da gwamnonin suka shigar mai lamba SC/CV/329/2025 tana da dalilai guda takwas da aka gina hujjojinta a kansu.
Gwamnatocin jihohin da suka shigar da ƙarar sun haɗa da: Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa.
Gwamnonin sun bukaci Kotun Koli da ta fayyace ko Shugaban Ƙasa na da ikon dakatar da tsarin dimokuradiyya na wata jiha ko babu.
Sannan sun bukaci kotun da ta tantance ko matakin da Shugaban Ƙasa ya ɗauka na ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers bai ci karo da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ba.
A cikin roƙon da gwamnonin suka shigar ta hannun Attoni-Janar na jihohinsu, sun bukaci kotun da ta fayyace:
Ko bisa ga tanadin sassa 1(2), 5(2), 176, 180, 188, da 305 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, Shugaban Ƙasa na da ikon dakatar da Gwamna da Mataimakin Gwamna na wata jiha kuma ya naɗa mutumin da bai fito daga zaɓe ba a matsayin mai gudanarwa na musamman, karkashin hujjar dokar ta-baci?
Ko bisa ga tanadin sassa 1(2), 4(6), 11(4) & (5), 90, 105 da 305 na Kundin Tsarin Mulki, Shugaban Ƙasa na da ikon dakatar da Majalisar Dokokin wata jiha a ƙarƙashin hujjar dokar ta-baci?
Ko barazanar da wanda ake ƙara, mai wakiltar Shugaban Ƙasa, ke yi cewa za a iya dakatar da gwamna da mataimakinsa bisa dalilin dokar ta-baci ba sabawa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ba ne?
Ana sa ran waɗanda ake ƙara a shari’ar za su gabatar da amsarsu cikin kwanaki 14 bayan an kai musu sammaci.
Sai dai wasu majiyoyi daga Kotun Koli da Ma’aikatar Shari’a sun shaida wa Jaridar The Punch cewa har yanzu ba a mika wa gwamnatin tarayya takardun ƙarar ba.
Wani lauya a Ma’aikatar Shari’a ya bayyana cewa, “Tun da muka ji labarin ƙarar, mun shirya amsar da za mu bayar. Mun ɗauki kwanaki uku muna bincike amma har yanzu ba a kawo mana sammaci ba.”