Connect with us

Featured

Sama Da Kashi 40% Na Likitocin Najeriya Su Na Aiki A Lagos Da Abuja Ne – Ministan Lafiya

Akalla likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya domin yin aiki a ƙasashen waje a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata, a cewar Ministan Lafiya da walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata 08 ga Afrilu 2025 a Abuja, yayin taron bita na shekara-shekara na Ƙungiyar Likitoci na Afirka (AMCOA), wanda Majalisar Likitoci da Masu kula da Hakori ta Najeriya (MDCN) ta shirya.

Ministan ya ce, yawan ficewar likitoci daga Najeriya baya rasa nasaba da dalilai na tattalin arziki, kyawawan yanayin aiki, da ingantattun cibiyoyin bincike a ƙasashen waje.

Ya kuma kara da cewa, gwamnati na aiki tukuru domin magance wannan matsala.

Ya ce, “Mun ninka yawan guraben horo a makarantu na likitanci, magani, jinya, da sauran fannonin kiwon lafiya. Domin ƙwarewarmu ta nuna cewa idan an horar da ƙarin ƙwararru da yawa na iya zama kuma waɗanda suka tafi sukan dawo.”

Ministan ya kuma ce gwamnati na aiki don magance matsalar rashin daidaito wajen rarraba ma’aikatan lafiya, inda ya bayyana cewa fiye da kashi 40% na likitocin ƙasar nan suna zaune ne a Legas da Abuja, yayin da yawancin sassan Najeriya ba su da wadatattun likitoci.

Ƙaramin Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dr. Iziaq Adekunle Salako, ya ce “Nahiyar Afirka na fuskantar manyan ƙalubale a fannin kiwon lafiya, ciki har da cututtuka masu yaɗuwa, ƙarancin kayan aiki, tsadar kula da lafiya, sauyin yanayi, matsin tattalin arziki, da ƙaura da ma’aikatan lafiya ke yi.”

Ya kara da cewa, Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da cewa ƙwararru a fannin lafiyar na bin ƙa’idojin kwarewa, ɗabi’a, da ladabi, domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da ingantaccen kula da marasa lafiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet