Connect with us

Featured

NDLEA Ta Kai Samame a Maɓoyar Ƴan Shaye-Shaye a Kano, Inda Ta Kama Mutane 22

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta kama mutane 22 da ake zargi dauke da miyagun ƙwayoyi iri-iri yayin samamen da ta kai a wurare daban-daban a faɗin jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kano.

Maigatari ya ce kama waɗanda ake zargin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da kwamandan jihar, Malam Abubakar Idris-Ahmad ke yi, domin yaƙi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi a jihar.

“A ranar 10 ga Afrilu, hukumar ta kai samame wasu wurare da ake sha da siyar da miyagun ƙwayoyi, da suka haɗa da Dan’agundi, yankin Gwangwazo, Farm Centre ta hanyar Zaria, Tashar Rami da Filin Idi a Kano,” in ji Muhammad Maigatari.

“Wannan aikin ya nuna jajircewar rundunar mu wajen yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma amfani da su, wanda ke ci gaba da zama barazana ga tsaron jama’a da lafiyar al’umma.”

Ya ƙara da cewa an kwato nau’o’in miyagun ƙwayoyi masu yawa irin su tabar wiwi (cannabis sativa), da kuma wasu muggan makamai na hannu da aka ƙera a gida.

Haka kuma ya ce, ana cigaba da bincike domin gano masu fataucin kwayoyin cikin waɗanda aka kama, kuma waɗanda aka samu da laifi a cikin su za a gurfanar da su a kotu.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet