Connect with us

Featured

Hisbah A Kano Ta Rushe Wajen Da Ake Rububin Zuwa Karbar Ruwan Magani

Hisbah A Kano Ta Rushe Wajen Da Ake Rububin Zuwa Karbar Ruwan Magani.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana dalilan ta na rushe wani wuri da ake bayar da wani ruwa a matsayin magani, wanda ke Hotoron Arewa a cikin birnin Kano.

Tun a kwanakin baya aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa an ga sawun ƙafar Annabi (SAW) a wajen, wanda dalilin hakan ya sa mutane su ka fara tururuwa zuwa wajen, domin a cewar sun ga wani irin sawun kafa a cikin ƙasa mai laushi, inda kuma ruwa ke fitowa daga wurin.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne cikin gaggawa, bayan samun rahotannin cewa jama’a da dama na zuwa wajen domin neman warakar cutuka da kuma samun tabarruki.

Da yake tabbatar da rushe wajen ga jaridar The PUNCH a ranar Laraba, Darakta-Janar na hukumar, Dr Abba Sufi, ya ce an rushe wurin ne a ranar Litinin.

“An rushe wurin ne a ranar Litinin bayan mun gano cewa wasu marasa kishin al’umma na amfani da wurin wajen yaudarar marasa lafiya da ke neman magani,” in ji shi.

Sufi ya kuma ja hankalin mazauna Kano da su yi watsi da duk wata magana da ke yaɗawa cewa wurin yana da tsarki ko kuma ruwan yana warkar da marasa lafiya.

 

 

 

 

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet