Featured
Rahoto: Adadin Talakawan Najeriya Zai Ƙaru Da A Shekarar 2027– Bankin Duniya

Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziƙi da kuma yanayin tsadar rayuwa a Najeriya, ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yiwa ƙawanya a Najeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027.
Rahoto da Bankin Duniya da ke fita bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya ce dogaro da Najeriya ta yi gabaɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba da tafiyar hawainiya.
Bankin na duniya ya ce har yanzu mahukuntan Najeriya ba su ɗauko hanyar fitar da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki talakawan ƙasar ba.
A cewar bankin abin takaici ne yadda talakawan ƙasashe masu tarin albarkatu ke fama da talauci saboda rashin mayar da hankali daga shugabanni.
Bankin ya ce duk da ci gaban da Najeriya ta samu a sauran fannonin da ba na man fetur ba musamman a bara, amma duk da haka babu alamar samun ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin talakawan ƙasar ta yammacin Afrika.
Rahoton ya jaddada cewa har yanzu yankin ƙasashen Sahel ne ke kan gaba a talauci a duniya gaba ɗaya, yayinda yankin ke da kaso 80 adadin mutane miliyan 695 na mutanen da ke fama da baƙin talauci.