Featured
Korafe-Korafen Jama’a Ya Sa Za Mu Sake Nazarin Sakamakon Jarabawar UTME Na Bana – JAMB

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta ce za ta sake duba Jarrabawar UTME ta shekarar 2025, bayan korafe-korafe daga mutane davdama kan matsalolin fasaha da tambayoyin da ba su cika ba, da kuma sakamakon ƙaramin maki ba kamar yadda aka saba ba.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Fabian Benjamin ya fitar, JAMB ta bayyana cewa ta karɓi “ƙorafe-ƙorafe da ba su saba ba” tun bayan fitar da sakamakon jarrabawar a ranar Jumma’ar da ta gabata.
Sanarwar ta ce wannan ƙoƙorafe-ƙorafen ne ya saka hukumar ta yanke shawarar yin bincike cikin gaggawa saɓanin yadda aka saba yi a baya.
An haɗa ƙwararru daga fannin kimiyyar kwamfuta da masu kimanta jarrabawa da shugabannin jami’o’i don taimakawa a aikin.
JAMB ta tabbatar da cewa idan aka gano wata matsala a tsarin, za a tabbatar an ɗauki matakan da suka dace nan take.