Connect with us

Featured

Tinubu Ya Bukaci Sojoji Su Yi Gaggawar Kawo Ƙarshen Matsalar Rashin Tsaro

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci dakarun sojojin Najeriya da su kara zage damtse wajen magance kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan.

Tinubu ya bayyana cewa ci gaban tattalin arziki na da alaka da tsaron kasa, yana mai bada umarnin cewa duk wanda ke barazana ga zaman lafiyar Najeriya a gaggauta yin maganin.

Shugaba Tinubu ya fadi hakan ne a yau Juma’a 16 ga Mayun, 2025, a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja,yayin bikin kaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu kirar Agusta 109 Trekker, a wani bangare na bukukuwan cikar shekaru 61 da kafa rundunar sojin saman Najeriya.

Shugaban, wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya jaddada cewa dole ne a karfafa tsaro domin ‘yan Najeriya su samu damar gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zamanantar da rundunar soji,tare da tabbatar da cewa an samar da kayayyakin aiki masu inganci don gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Ya kuma bukaci sojoji su kasance cikin shiri domin tunkarar kalubalen tsaro da ke wajen iyakokin Najeriya ta hanyar shiga ayyukan samar da zaman lafiya a duniya.

Shugaban ya bukaci rundunar sojin sama da ta tabbatar da kwarewa da kula da kayan aiki a lokacin da ake amfani da su.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet