Featured
Kwankwaso Ya Fita Daga Jam’iyyar Mu Tun 2023 – Shugaban NNPP Na Ƙasa

Shugaban Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Na Ƙasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba mamba bane a cikin jam’iyyar su a halin yanzu.
Da yake magana a shirin Daily Politics na Trust TV, Dr. Gilbert ya ce jam’iyyarsu ba ta da wata alaƙa da Kwankwaso tun bayan da ya yanke alaka da jam’iyyar a shekarar 2023.
A cewar sa, “Bari na yi muku dalla-dalla : akwai batutuwa masu mahimmanci da ya kamata a tattauna fiye da Kwankwaso. Ban zo nan in tattauna shi ba. Ya zama tarihi a jam’iyyar NNPP. Ya taɓa zama ɗan jam’iyyar, daga baya kuma ya fice tare da ƙungiyar sa ta Kwankwasiyya. Saboda haka bana son in cigaba da magana a kansa.
“Ya fita daga jam’iyyar bisa tanadin kundin tsarin mulkin NNPP da kuma hukuncin da wasu kotuna suka yanke – kamar yadda kotun babban birnin tarayya (FCT) da kuma kotun jihar Abia suka tabbatar.”
Da yake tsokaci game da sauya sheƙa da ke faruwa cikin manyan jam’iyyun adawa da suka haɗa da NNPP, Gilbert ya ce, “Kwankwaso ya shigo da mutanensa – wato tafiyar Kwankwasiyya. Idan ka duba tarihin waɗanda suka bar jam’iyyar, zaka fahimci cewa su mambobi ne na Kwankwasiyya. Su ne suka taka rawar gani wajen nasarar NNPP a Kano.”
Ya ƙara da cewa mutanen da suka bar jam’iyyar sun fi samun matsala da tafiyar Kwankwasiyya, ba da NNPP kanta ba.
“Ina so in jaddada cewa waɗanda suka fice ba su fice daga NNPP ba. Muna da hulɗa da su. Suna gaya mana cewa ‘muna tare da ku, ba mu da matsala da jam’iyyar ko shirye-shiryenta, amma muna da matsala da tsarin tafiyar da aka shigo da ita cikin jam’iyyar wato Kwankwasiyya, wanda muka ci zaɓe ta cikinta’.”
“Eh, mun rasa Sanata – Kawu – da wasu ‘yan majalisa biyu, amma wannan ba juyin juya hali bane a kan NNPP.”
“Mutane sun gaji. Suna gaya wa Kwankwasiyya cewa ‘mun gaji da yadda kuke tafiyar da al’amura. Abu ya zama na mutum ɗaya kawai’. Amma suna tare da mu har yanzu. Muna da alaƙa da su.”
Ya ce ɗabi’ar dimokuraɗiyya na bai wa ‘yan siyasa ‘yancin sauya sheƙa idan sun gaji da inda suke.
“Suna da ‘yancin barin inda suka fi jin damuwa. Amma na jaddada: waɗannan mutane ba su fice daga NNPP ba. Abin da suka fice daga shi shine tafiyar Kwankwasiyya.”
Ya ƙara da cewa, “Waɗannan mutane da muke da kyakkyawar alaƙa da su ba su da matsala da shugabancin jam’iyyar NNPP. Matsalarsu tana cikin yadda tafiyar Kwankwasiyya ke tafiya.”
Da aka tambaye shi game da raɗe-raɗin shigar Kwankwaso jam’iyyar APC, ya ce, “Zai iya shiga inda ya ga dama, domin ba mu da wata alaƙa da shi. Ya bar jam’iyyar mu tun watan Yuni 2023.”