Connect with us

Featured

Dokar Tilasta Yan Najeriya Yin Zaɓe Ya Tsallake Karatu Na Biyu

Yan majalisar dokoki a Najeriya sun sake zama inda suka yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar nan da ke neman yin gyaran fuska ga dokar zaɓe ta 2022 da za ta tilasta ‘yan ƙasar jefa ƙuri’a a lokacin manya da ƙananan zaɓuka masu zuwa.

Wannan sabon ƙudurin doka dai ya janyo rarrabuwar kai a majalisar dokokin Najeriyar.

Yayin da wasu ƴan majalisar ke ganin zai zama tamkar take ‘yancin ‘yan ƙasar ne, wasu kuwa na bayyana shi a matsayin mataki mai kyau, wanda idan ya zama doka za a iya cin tara ko kuma yanke masa hukuncin zaman gidan kaso duk wanda ya ƙi yin zaɓe.

‘Yan majalisar dokokin sun gudanar da muhawara tare da tattaunawa game da shirin yin gyaran fuska ga dokar shekarar 2022 da ta shafi zabe domin tabbatar da kowane dan Najeriya ya sauke nauyin da ke kansa na yin zabe.

Sun bayyana cewa akwai bukatar cin tarar naira dubu 100 ga duk wanda ya ki jefa kuri’a ko kuma dauri a gidan yari na tsawon watanni shidda ko ma duka biyu.

‘Ƴan majalisar dai sun kai ga yi wa kudurin karatu na farko da na biyu, wanda kuma kakakin majalisar wakilan Tajudeen Abbas ya jagoranci zaman.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet