Featured
NDLEA Ta Kama Masu Ɗaukar Nauyin Mahajjata A Kano Domin Safarar Ƙwayoyi Zuwa Saudiyya

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta bankado wata kungiyar masu laifi dake amfani da mahajjata a matsayin masu safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudiyya, inda ta kama manyan shugabanninta guda uku a Kano.
Shugabannin ƙungiyar, Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Tijjani, da Muhammad Aji Shugaba, an kama su ne a ranakun Talata da Laraba, 27 da 28 ga Mayu, bayan kama wasu mahajjata biyu a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano ɗauke da kunshin cocaine guda 90.
A cewar sanarwar da Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a yau Lahadi 02 ga Mayun 2025, ya ce an kama mahajjatan biyu, Ibrahim Mustapha da Muhammad Shifado, a lokacin da suke shirin hawa jirgin Ethiopian Airlines ET 940 zuwa Jeddah.
Babafemi ya ce, bayan samun bayanan sirri, jami’an NDLEA sun binciki jikin waɗanda ake zargi ta hanyar na’urar duba ciki, inda aka gano sun haɗiye miyagun ƙwayoyi. Bayan sanya su karkashin lura ta musamman ne suka fitar da ƙunshi 45 kowannensu, jimillar 90 mai nauyin 1.04kg.
“Bincike ya tabbatar da cewa shugabannin wannan muguwar ƙungiya su ne waɗanda ke ɗaukar nauyin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudiyya. Bayan haka, jami’an NDLEA sun gudanar da gaggawar samame inda aka kama Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Muhammad Tijjani, da Muhammad Aji Shugaba a Kano a ranakun 27 da 28 ga Mayu,” a cewar sanarwar.