Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso Ƴan Najeriya Daga Isra’ila da Iran Sakamakon Rikicin Da Ke Ƙara Ta’azzara

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye domin fara kwaso ‘yan Najeriya wadanda suka makale a kasashen Isra’ila da Iran, sakamakon rikicin da ke kara tsananta tsakanin kasashen biyu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a daren Talata 17 ga Yuni 2025, ya bayyana cewa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Tel Aviv da Tehran na ci gaba da tuntubar ‘yan Najeriya da abin ya shafa tare da hada kai da su domin tabbatar da dawo da su Najeriya cikin aminci.

An bukaci ‘yan Najeriya da ke cikin yankunan da rikicin ya shafa da su kiyaye doka da tsare-tsaren tsaro na cikin gida tare da tuntubar ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa da su don yin rajista da samun karin bayani.

Ma’aikatar ta yaba da kokarin jami’an diflomasiyyar Najeriya da ke kasashen biyu saboda jajircewarsu da sadaukarwarsu wajen kare ‘yan Najeriya a wadannan lokuta masu wahala.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da cewa, bayan tsanantar rikicin da ke tsakanin Kasar Isra’ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a wadannan kasashe.

“Don haka ana shawartar duk ‘yan Najeriya da abin ya shafa da su tuntubi ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa da su don rajista da kuma samun karin bayani.

“Ma’aikatar ta yaba da kokarin da ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Tel Aviv da Tehran ke yi wajen kula da ‘yan Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

“Muna tabbatar wa da al’umma cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nan daram wajen kare lafiyar ‘yan kasa, a gida da kuma kasashen waje, tare da hadin gwiwa da hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa domin tabbatar da tsaro da dawo da su cikin lokaci.”

Ma’aikatar ta jaddada matsayin Najeriya na goyon bayan warware rikice-rikice ta hanyar lumana da kuma daukar matakin zaman lafiya a yankunan da ma duniya baki daya.

Sanarwar ta ce: “A wannan lokaci, Gwamnatin Najeriya na sake yin kira da a dakatar da duk wani farmaki da ya ke gudana, ta na kuma bukatar dukkan bangarorin da abin ya shafa da su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma fifita kare lafiyar fararen hula.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet