Featured
Isra’ila da Hamas Za Su Sake Tattaunawa a Masar

Masu shiga tsakani daga Isra’ila da Hamas za su gudanar da muhimman tattaunawar ƙeƙe-da-ƙeƙe a ƙasar Masar a ranar Litinin 06 ga Oktoba, da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ya daɗe yana gudana a Gaza. Wannan ganawa na zuwa ne bayan da Hamas ta amince da wasu sassa na shirin zaman lafiya da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.
Rahotanni sun nuna cewa akwai muhimman abubuwa da dama cikin yarjejeniyar da ke buƙatar tattaunawa kafin cimma matsaya ta ƙarshe. Masu nazari sun bayyana damuwa cewa kowane ɓangare na iya sauya matsayarsa a yayin ganawar, lamarin da ke sa fargabar cewa tattaunawar na iya yin rauni ko ma ta rushe gaba ɗaya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an samu ci gaba a tattaunawar da aka yi a ƙarshen mako kan sakin sauran mutanen da Hamas ke riƙe da su. Ya bayyana hakan ne a wani jawabi, inda ya nuna gamsuwa da irin tattaunawar da aka gudanar tsakanin ɓangarorin biyu.
Trump ya kuma yi kira ga Isra’ila da Hamas da su yi gaggawar cimma matsaya, yana mai gargaɗin cewa rashin fahimtar juna na iya haifar da sakamako mai tsanani. Ya ce duniya na sa ran ganin ƙarshen rikicin Gaza cikin gaggawa ta hanyar yarjejeniya mai ɗorewa.