Connect with us

Featured

Iska Mai Ƙarfi Ta Yi Ajalin Mutane 5 Tare Da Lalata Gidaje Sama Da 1,400 A Sokoto

Wata iska mai ƙarfi da ta faru a ƙananan hukumomin Gwadabawa da Kware a Jihar Sokoto ranar Talata sun yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata daruruwa da kuma janyo mummunar barna a yankunan biyu.

Jami’an Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Sokoto (SEMA) tare da na Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun gudanar da cikakken bincike kai tsaye a wuraren da abin ya shafa a ranar Asabar 21 ga Yuni, 2025, inda suka bayyana irin asarar da al’umma suka tafka.

Rahoton binciken ya nuna cewa hadarin ya shafi gidaje sama da 1,400 da kuma gine-ginen gwamnati da na jama’a, ciki har da makarantu da wasu muhimman wuraren ayyuka.

A cewar rahoton, a ƙaramar hukumar Gwadabawa kadai, gidaje 878 ne suka lalace, wanda hakan ya shafi gidaje 1,306 tare da raba mutane kimanin 7,836 da matsuguni.

“Mutane goma sha ɗaya sun jikkata da matsanancin rauni. Haka kuma an tabbatar da mutuwar mutane biyar a unguwar Marabawa, ciki har da yara biyu ‘yan shekara ɗaya da rabi da kuma shekara uku, ‘ya’yan Mansur Salihu Talhi,” inji rahoton.

Ƙungiyar da ta jagoranci binciken a Gwadabawa sun haɗa da DPM Shehu Muhammad, Kansilan Gidan-Kaya Hon. Siba Sodangi, dattijo Adamu Abdullahi Talhi, da jami’in SEMA Nafi’u Bello.

A ƙaramar hukumar Kware kuwa, SEMA ta ce gidaje 523 ne suka rushe, lamarin da ya shafi gidaje 1,403 tare da jikkatar mutane 18.

“Gine-ginen gwamnati da dama sun samu mummunar illa, ciki har da makarantar sakandare ta gwamnati dake Kware, inda ajujuwa suka rushe.

“Ƙaramar unguwar Kofar-Barga na daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni, inda gidan wani mazaunin garin mai suna Ahmad Abbas ya rushe baki ɗaya.

“Haka zalika, fiye da gidaje 100 ne suka lalace a yankin 30-Quarters na garin.”

SEMA ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattara bayanan mutanen da abin ya shafa da kuma kadarorin da suka lalace.

A cewar hukumar, “Za a mika bayanan ga gwamnatocin jiha da na tarayya domin a gaggauta kai dauki ga waɗanda abin ya shafa.”

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet