Featured
Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki a Janairu 2026 – Gwamnatin Tarayya

Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa, Zacch Adedeji, ya bayyana cewa sabbin dokokin gyaran haraji da shugaba Tinubu ya sanya hannu a kansu za su fara aiki ne daga 1 ga Janairu, 2026.
Adedeji ya ce wannan matakin zai ba gwamnati damar shafe watanni shida tana tsara hanyoyin aiwatarwa, wayar da kai da kuma tsarin kasafin kuɗi na shekara.
Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis 26 ga Yuni, 2025. Ya ce, “Dangane da yadda ake gudanar da irin waɗannan sauye-sauye a duniya, ana buƙatar lokaci domin duk masu ruwa da tsaki – kamfanoni, ‘yan kasuwa, da hukumomi – su daidaita tsarin su.”
Ya cigaba da cewa, “Saboda haka, da yardar majalisar dokoki da kuma shugabancin shugaban ƙasa, ranar da sabbin dokokin za su fara aiki za ta kasance 1 ga Janairu, 2026, in sha Allah.”
Adedeji ya jaddada muhimmancin fara aiwatar da sauye-sauyen haraji tun daga farkon shekara, inda ya ce, “Ba daidai ba ne a fara irin wannan sauyi tsakiyar shekara. Idan ana so a aiwatar da doka yadda ya kamata, kamata ya yi a fara daga farkon shekara.”
Ya ƙara da cewa wannan jadawalin zai ba da damar isasshen shiri, wayar da kai da kuma daidaita tsarin kasafin kuɗi na gwamnati.