Connect with us

Featured

Cire Tallafin Mai Abu Ne Da Ya Zama Dole – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa jawabin cire tallafin mai da ya yi a ranar rantsar da shi lamari ne mai matukar zafi, amma hakan ya zama tilas ne domin ceto tattalin arzikin ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙasa, Mohammed Idris Malagi, ya sake jaddada wannan matsaya ta shugaban ƙasa a taron Gwamnonin Jam’iyyar APC da Kwamishinonin Yaɗa Labarai daga jihohin jam’iyyar, wanda aka gudanar a birnin Minna.

Ya buƙaci kwamishinonin da su samu sahihan bayanai da ƙididdiga domin jama’a a faɗin ƙasar su fahimci waɗannan sauye-sauye da shirye-shirye, su kuma san yadda za su amfana da su.

“ Ɗaya daga cikin mafi ƙalubale da muhimmiyar doka da wannan gwamnati ta ɗauka ita ce cire tallafin mai, mataki ne mai zafi amma tilas ne domin ceto tattalin arzikin ƙasa daga rugujewa.” in ji Malagi.

“Cire tallafin ya ba da damar ƙarin kuɗi wajen gina manyan ababen more rayuwa kamar su titin gabar teku na Lagos zuwa Calabar, titin Sokoto zuwa Badagry, Calabar zuwa Abuja, da titin jirgin ƙasa mai layi guda na Kaduna-Kano, da kuma hanyar Abuja-Kaduna-Kano.”

Malagi ya ce nauyin da ya rataya kan kwamishinonin yada labarai shi ne su wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar nan, su kuma sanar da su irin waɗannan sauye-sauye da yadda za su amfana da su.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet