Featured
Afrika Na Asarar Dala Biliyan $90 Duk Shekara Sakamakon Rashin Wadatattun Matatun Mai a Nahiyar – Dangote

Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya bayyana cewa nahiyar Afrika na asarar akalla dala biliyan 90 a kowace shekara saboda shigo da man fetur mara inganci, sakamakon rashin wadatattun matatun mai a nahiyar.
Dangote ya bayyana hakan ne a yayin taron West African Refined Fuel Conference da ake gudanarwa a Abuja, inda ya ce rashin isassun matatun mai a nahiyar ya sa Afrika ke shigo da fiye da tan miliyan 120 na man da aka tace daga kasashen waje a duk shekara.
Taron wanda Hukumar Kula da Harkokin Tsakiya da Na Ƙasa (NMDPRA) ta shirya tare da S&P Global Commodity Insights, na da nufin samar da daidaitaccen tsarin farashin man fetur a yankin.
Dangote ya yabawa Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) bisa samar da wasu jiragen daukar man ga matatar Dangote tun daga fara tace mai. Amma ya bayyana cewa kamfaninsa na shigo da gangar danyen mai miliyan 9 zuwa 10 a kowane wata daga Amurka da sauran kasashe.
Ya ce: “A halin yanzu, muna sayen danyen mai tsakanin miliyan 9 zuwa 10 a kowane wata daga Amurka da wasu kasashen waje. Ina mika godiya ga NNPC bisa samar mana da wasu jiragen daukar mai tun daga lokacin da muka fara tacewa har zuwa yanzu.”
Dangote ya kara da cewa duk da cewa Afrika na fitar da fiye da gangar danyen mai miliyan 7 a rana, ba a tace fiye da kashi 40% na man da ake bukata a gida ba, alhali kasashen Turai da Asiya na tace fiye da kashi 95% na man da suke bukata.
“Yayin da muke fitar da danyen mai da yawa, muna kuma shigo da tan miliyan 120 na man da aka tace daga waje. Wannan yana nufin muna fitar da ayyukan yi tare da shigo da talauci cikin nahiyar. Wannan kasuwa ce da ta kai dala biliyan 90 da muke bai wa kasashen da suka fi mu karfi wajen tace mai.”
Dangote ya jaddada cewa wannan al’amari ba ya da tushe ko amfani a tattalin arziki, domin Afrika tana da damar tace man a gida ba sai ta fita da shi ta dawo da shi daga waje ba.