Connect with us

Featured

Yara 400,000 Na Fuskantar Barazanar Mutuwa a Najeriya Sakamakon Yunwa – UNICEF

Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa yara miliyan 3.5 a Najeriya na fama da matsanancin yunwa (severe acute malnutrition).

UNICEF ya bayyana hakan ne a jiya Talata 22 ga Yuli, inda ya ce yara 400,000 na iya mutuwa cikin wata ɗaya da kwana takwas muddin ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Shugabar Sashin Ayyuka da Ƙididdiga na UNICEF a Najeriya, Judith Leveille, ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja, dangane da goyon bayan Tarayyar Turai ga waɗanda rikicin Yelewata ya shafa a Jihar Benue da kuma gaggawar matsalar abinci a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

A cewar Leveille: “Najeriya na fuskantar barazanar ƙarancin kayan abinci masu gina jiki da ake amfani da su wajen jinya ga yara masu matsanancin yunwa. A yanzu haka, akwai haɗarin cewa za mu samu ƙaranci kafin 1 ga watan Satumba.”

A cewar ta, idan hakan ya faru, fiye da yara 400,000 za su mutu – waɗanda da dama daga cikinsu na iya zama fitattun masana, ’yan fim, mawaka, ko ma masu lashe kyautar Nobel a gaba.

“Najeriya na da damar fitar da irin waɗannan mutane. Amma yanzu muna da wata guda da kwana takwas don hana mace-macen da za a iya kaucewa. Ina nufin abinci irin su ready-to-use therapeutic food,” in ji ta.

Ta ce a halin yanzu akwai asibitocin gyaran lafiya da ke cike da yara da ke buƙatar kulawa ta gaggawa.

 

 

 

 

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet