Connect with us

Featured

Gwamnatin Tinubu Bata Watsar Da Yankin Arewa Ba — Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata ikirarin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi cewa an watsar da Arewa a mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Kwankwaso ya bayyana ra’ayinsa ne a wani taron tattaunawa kan sauya kundin tsarin mulki na 2025 da aka gudanar a Kano, inda ya ce ana karkatar da dukiyar ƙasa zuwa kudanci, lamarin da ke ƙara jefa Arewa cikin talauci da rashin tsaro.

Ya kuma koka da yanayin titunan tarayya a jihohin Arewa, yana misalta tafiyarsa daga Abuja zuwa Kano ta hanya a maimakon jirgi — sakamakon soke tashi — a matsayin “azaba” saboda lalatattun hanyoyi.

Amma da yake maida martani a ranar Juma’a a shafinsa na X, mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce zargin Kwankwaso ba daidai ba ne.

“Zargin cewa an watsar da Arewa ba gaskiya ba ne. Gwamnatin Tinubu ta fara da ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka da dama a Arewa, ciki har da tituna, noma, lafiya da makamashi,” in ji Dare.

Dare ya bayyana muhimman ayyuka da shirye-shirye da ake aiwatarwa a Arewa da ke nuna jajircewar gwamnatin wajen bunƙasa yankin.

Ya ambaci ayyuka kamar Abuja–Kaduna–Kano Expressway, Sokoto–Badagry Super Highway, da Ajaokuta–Kaduna–Kano Gas Pipeline.

Har ila yau, ya ambaci shirin Agriculture Value Chain da darajarsa ta kai dala miliyan $158.15 a jihohi tara na Arewa, da kuma Kolmani Integrated Development Project a Bauchi da Gombe.

Akwai kuma shirin ACReSAL da ke ƙoƙarin dawo da sama da hekta miliyan ɗaya na ƙasar da ta lalace.

A fannin lafiya, Dare ya lissafa Asibitin Koyarwa na ABU Zaria, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, da Cibiyar Lafiya ta Tarayya a Nguru, da kuma sabunta fiye da cibiyoyin lafiya na matakin farko 1,000 a Arewa.

A fannin hanyoyi, akwai ayyuka kamar Kano–Kongolam Road, Kaduna–Jos Road, Kano–Maiduguri Dual Carriageway, da gyaran hanyoyi a Borno da Adamawa.

Game da makamashi, Dare ya ambaci bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (614 km), Gwagwalada Power Plant, da ayyukan hasken rana a Kaduna.

A fannin jiragen ƙasa kuwa, ya ambaci layin jirgin ƙasa na Kaduna–Kano, layin Kano–Maradi, da kuma gyaran Jirgin Abuja Metro.

“Arewa ba a bar ta a baya ba. Daga tituna zuwa bututun gas, noma, lafiya da jiragen ƙasa — wannan gwamnati na kula da Arewa sosai,” in ji shi.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet