Connect with us

Featured

NDLEA Ta Kama Tramadol Da Yawanta Ya Kai Biliyan 1.3 A Cikin Watanni 18 – Marwa

Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (rtd), ya bayyana cewa hukumar ta kama kwayoyi da suka hada da kwayoyin Tramadol biliyan 1.3 da robar Codeine miliyan 4.4 daga watan Janairu 2024 zuwa Yuni 2025.

Marwa ya bayyana hakan ne a lokacin wani zama na tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan kasa da aka gudanar na tsawon kwanaki biyu a Kaduna.

Ya danganta wannan gagarumar nasara da goyon bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke bai wa hukumar.

A cewarsa: “Daga watan Janairu 2024 zuwa Yuni 2025, mun kama robar codeine fiye da miliyan 4.4.

Mun kuma kama kwayoyi nau’in opium da ake kira Tramadol fiye da biliyan 1.3.

Kwaya daya ta Tramadol yanzu ana sayarwa a kan naira 1,000. Wannan yana nufin darajar kasuwa na kwayoyi biliyan daya na iya kaiwa kusan naira tiriliyan daya.

Ku yi tunanin irin makaman da ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga za su iya saya da wannan kudi ko kuma irin illar da biliyan daya na kwayoyin Tramadol za su iya yi idan suka shiga hannun jama’a.”

Marwa ya ci gaba da cewa tun da Tinubu ya hau mulki a 2023, NDLEA ta kama kwayoyi da su ka kai tan 5,555, wanda yayi daidai da manyan motoci 200 na kaya.

“Ku yi tunanin manyan motoci 200 dauke da miyagun kwayoyi suna yawo a titunanmu.

Haka zalika, mun kama ‘yan kwaya 2,000, mun gurfanar da 8,682, kuma mun yi wa fiye da 24,000 jinya da gyaran hali.”

NAN

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet