Featured
Gwamnatin Kano da UBEC Sun Yi Haɗin Gwiwa Domin Kawo Karshen Matsalar Yaran Da Basa Zuwa Makaranta

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na yakar matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Ilimin Firamare ta Ƙasa (UBEC).
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a ranar Juma’a 01 ga Agusta, lokacin da ya karɓi shugabannin UBEC ƙarƙashin jagorancin Sakatare Janar na hukumar, Dr Aisha Garba, a gidan gwamnatin Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar, ziyarar ta bayyana haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kano domin gyara tsarin ilimin firamare gaba ɗaya.
Gwamna Yusuf ya ce jihar tana ƙara zuba jari sosai wajen gina makarantu, samar da kujeru da tebura, kayan koyo da koyarwa da kuma kyautata muhallin koyo domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi.
“Muna da manufa guda, mai matuƙar muhimmanci — fitar da kowanne yaro daga titi zuwa aji. Muna aiki kafada da kafada da UBEC da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin wannan buri ya zama gaskiya,” in ji gwamnan.
A nata bangaren, Dr Garba ta yaba da ci gaban da Jihar Kano ke samu a fannin sauya fasalin ilimi, tana mai bayyana jihar a matsayin wadda ke jagorantar yaki da jahilci.
“Kano na ɗaukar matakai masu ƙarfi. Karkashin jagorancin Gwamna Yusuf da goyon bayan UBEC, muna da yakinin cewa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta zai ragu sosai,” in ji ta.