Connect with us

Featured

SERAP Ta Bawa Gwamnan Jihar Neja Awanni 48 Ya Buɗe Badeggi FM

Kungiyar kare hakkin dan Adam da tabbatar da gaskiya a shugabanci, wato SERAP, ta bai wa Gwamna Umar Bago na Jihar Neja wa’adin awanni 48 domin ya janye umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM 90.1 da ke Minna, babban birnin jihar.

A cikin wata budaddiyar wasika da ta aike ranar 2 ga Agusta, wadda mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, kungiyar ta bukaci gwamnan da ya dawo da lasisin gidan rediyon, ya janye barazanar rushe ginin sa, tare da daina nuna bambanci da kuma tsangwama ga mai gidan, Shuaibu Badeggi.

SERAP ta ce, “Zarge-zargen da ba su da tushe da kuka yi na cewa gidan rediyon na ‘zuga tashin hankali’ wani yunkuri ne kawai na dakushe karsashin gidan rediyon da kuma hanashi fadin gaskiya.”

A baya dai, Gwamna Bago ya umurci Kwamishinan ‘yan sanda da na tsaro na cikin gida su rufe gidan rediyon, su soke lasisin sa, su kuma rushe ginin sa.

An kuma ruwaito cewa gwamnan ya bada umarni a binciki tarihin mai gidan bisa zargin cewa shirye-shiryen gidan na caccakar gwamnati da tada zaune tsaye.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet