Connect with us

Featured

Masu Amfani da MTN da Airtel Sun Kashe Naira Tiriliyan 2.5 Wajen Kira da Sanya Data Acikin Watanni 6

Masu amfani da layukan MTN da Airtel sun kashe jimillar Naira tiriliyan 2.53 wajen amfani da sabis na kira da intanet a cikin rabin farko na shekarar 2025, wanda ke nuna karin kashi 50.9% idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 1.68 da aka kashe a rabin farko na shekarar 2024.

Wannan na kunshe ne a cikin rahotannin watanni shida na farkon 2025 da kamfanonin sadarwar suka fitar.

Rahoton ya nuna yadda kashe kudin jama’a kan sadarwa ke karuwa, saboda sabon tsarin farashi, karuwar yawan wayoyin zamani, da kuma zuba jari a hanyoyin sadarwa da kamfanonin biyu ke yi.

MTN Nigeria

MTN ta samu kudin shiga har Naira tiriliyan 2.12 daga sabis na kira da intanet tsakanin Janairu zuwa Yuni 2025 — karin kashi 55.7% idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 1.36 a 2024.

Kudin da aka samu a Data: Naira 1.23tn (+69.2%)

Kudin da aka samu a kira: Naira 887.13bn (+40.3%)

Masu amfani da intanet: sun karu da kashi 11.8% zuwa miliyan 51

Jimillar masu amfani da layi: miliyan 84.7 (+6.7%)

Amfanin intanet na kowane mutum a wata: 13.2GB (+26.3%)

Yawan amfani da wayoyin zamani: 62.6%

Sabbin farashi da aka aiwatar a rubu’in biyu na shekara sun taimaka wajen bunkasa kudaden shiga. Haka zalika, MTN ta koma samun riba daga asarar N519.1bn a 2024 zuwa riba ta N414.9bn a 2025.

Airtel Nigeria

Airtel ta samu $298 miliyan (kimanin N412.43bn) daga sabis na kira da intanet a watanni shida na farko na 2025 — karin kashi 30.1% daga N316.94bn a 2024.

Kudin da aka samu a Data: Naira 226.98bn (+40.2%)

Kudin da aka samu a kira: Naira 185.46bn (+19.1%)

Masu amfani da intanet: miliyan 29.3 (+11.3%)

Amfanin intanet kowane mutum a wata: 9.3GB (daga 7.3GB)

Wayoyin zamani: 51.4%

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet