Featured
Sau 430 Gobara Ta Tashi a Neja a 2025 – Hukumar Kashe Gobara

Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa reshen jihar Neja ta bayyana cewa an samu gobara 430 a sassa daban-daban na birnin Minna tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2025. Kwamandan hukumar a jihar, AC Alikali Mohammad, ne ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce jami’an hukumar sun rika kai dauki cikin gaggawa zuwa wuraren da gobarar ta tashi, inda suka yi nasarar ceto rayuka da dukiyoyi da darajarsu ta kai biliyoyin naira. Ya kuma yaba da hadin gwiwar da ke tsakaninsu da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Neja wajen rage illar gobara.
Alikali ya ce hukumar na shirya Makon Wayar da Kan Jama’a kan kare kai daga Gobara a karshen kowace shekara domin ilmantar da jama’a. Sai dai ya nuna damuwa kan sakacin jama’a da rashin sanin lambobin gaggawa, yana mai kira ga al’umma su bi ka’idojin kariya da kuma ba da sahihin bayani ga hukumar.