Featured
Umarnin Kotu Ba Zai Dakatar Da Mu Daga Shiga Yajin Aiki Ba – Likitoci

Kungiyar Likitocin Koyon Aiki ta Najeriya (NARD) ta jaddada aniyarta ta fara yajin aiki a 12 ga Janairu, 2026, duk da umarnin Kotun Kwadago ta Kasa da ya hana daukar matakin. Shugaban NARD, Dr. Mohammad Suleiman, ya ce Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) ne kaɗai zai iya dakatar da yajin aikin.
Kotun Kwadago da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi da ke hana NARD da wasu shugabanninta shiga yajin aiki, bayan ƙarar da Gwamnatin Tarayya da Antoni Janar suka shigar. Sai dai Suleiman ya ce umarnin kotun bai girgiza mambobin ƙungiyar ba, yana zargin gwamnati da rashin nuna gaskiya duk da yarjejeniyar da aka cimma a Nuwamba 2025.
Ya kara da cewa har yanzu ana tattaunawa da gwamnatin tarayya, yana fatan a samu maslaha kafin karshen mako. A halin da ake ciki, reshen NARD na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH) ya sanar da cikakken goyon bayansa ga yajin aikin, yana mai cewa gwamnati ta kasa aiwatar da abubuwan da aka amince da su.