Connect with us

Featured

Likitoci Sun Janye Yajin Aiki a Najeriya

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana gudanarwa. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Muhammad Sulaiman, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X, bayan zaman majalisar zartarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da yajin ne na tsawon mako huɗu, bayan cimma wasu muhimman yarjejeniyoyi da gwamnatin tarayya game da buƙatun ƙungiyar guda 19. Daga cikin manyan matsalolin da aka fara warwarewa har da batun biyan kuɗin ƙarin matsayi, bashin albashi da ake binsu, da kuma alawus na musamman.

Kakaki24 ta gano cewa ƙungiyar na sa ran gwamnati za ta kammala biyan wadannan muhimman hakkoki cikin makonni biyu masu zuwa, domin magance matsalolin da suka haddasa yajin. NARD ta ce dakatarwar ba ƙarshen yajin ba ne, sai dai dama ga gwamnati ta cika alkawuranta.

Yajin aikin da likitocin suka yi ya jefa wasu asibitoci cikin tsaiko mai tsanani, inda marasa lafiya suka dinga korafin rashin samun likitoci, lamarin da ya yi barazana ga lafiyar al’umma a sassa daban-daban na ƙasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet