Featured
Ƙungiyar Likitoci Ta NARD Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ta Shirya Tsunduma

Kungiyar Likitoci na Najeriya (NARD) ta sanar da dage yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar na tsawon makonni biyu. Matakin ya biyo bayan shiga tsakani kai tsaye da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, tare da alkawurra daga muhimman masu ruwa da tsaki.
A wata sanarwa da Babban Sakataren NARD, Dr. Shuaibu Ibrahim, ya sanya wa hannu bayan taron gaggawa na NEC ta yanar gizo, kungiyar ta ce ta amince baki daya da dakatar da fara yajin aikin TICS 2.0. Ta ce dakatarwar ta kasance ta wucin gadi ne domin a sake tantance ci gaban tattaunawa a taron NEC na gaba da zai fara ranar 25 ga Janairu, 2026.
NARD ta bayyana kwarin gwiwar cewa shiga tsakani na Mataimakin Shugaban Kasa zai kawo mafita mai dorewa ga matsalolin bangaren lafiya. Haka kuma, ta ce an aiwatar da rahoton kwamitin da Ma’aikatar Lafiya ta kafa kan likitoci biyar na FTH Lokoja, tare da mika jerin bashin CONMESS kashi 25/35 cikin 100 zuwa IPPIS.