Featured
Zaben 2027 : Gwamnonin APC Na Kudu-Maso-Gabas Sun Sha Alwashin Kawowa Tinubu Yankinsu

Gwamnonin jam’iyyar APC na jihohin Imo, Enugu da Ebonyi, tare da shugabannin jam’iyyar a Kudu maso Gabas, sun amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin wa’adi na biyu a zaben 2027. Sun dauki wannan matsaya ne a taron masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar a otal din Presidential da ke Enugu.
Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya ce yankin ba zai iya ci gaba da kasancewa a keɓance a siyasar kasa ba, yana mai cewa siyasa tana bukatar hadin kai da dabaru. Ya tunatar da cewa Kudu maso Gabas ta ba APC kaso kadan a zaben 2023, lamarin da ya rage karfin tasirinta a matakin kasa, duk da cewa jam’iyyar na kara samun karfi a yankin.
A bangare guda, Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya bayyana goyon bayan a matsayin sauyin tunani mai amfani, yana danganta shi da ayyukan gwamnatin tarayya kamar farfado da layin dogo na Gabas da fadada filin jirgin saman Enugu. Sai dai tsohon shugaban PFN a Rivers, Apostle Eugene Ogu, ya soki matakin, yana cewa bai dace a goyi bayan Tinubu ba alhalin Nnamdi Kanu na tsare, yana mai cewa yankin bai samu gamsasshen kulawa daga gwamnatin tarayya ba.