Featured
Ƴansanda Sun Kama Ƴan Fashi 10 a Jigawa

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutane goma a wasu samame da ta gudanar a fadin jihar, domin dakile fashi da makami, dillancin miyagun kwayoyi da sauran laifuka. Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Litinin.
Ya ce samamen ya kai ga cafke wani da ake nema ruwa a jallo kan fashi da makami da wasu mutane tara, tare da kwace miyagun kwayoyi guda 7,028. Daga cikin wadanda aka kama akwai mutane bakwai da ake zargi da safarar ko amfani da kwayoyi, inda aka kwato sinadarai da ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.
’Yan sandan sun kuma kwato babur da aka sace a Hadejia tare da mayar da shi ga mamallakinsa, sannan sun gano shanu biyu da ake zargin an sace a Malam-Madori. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike da farautar wadanda suka tsere, tana kuma kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai domin yakar aikata laifuka a jihar.