Featured
Babu Wata Gwamnati Da Za Ta Iya Magance Dukkan Matsaloli – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ko da gwamnatin Bola Tinubu za ta yi shekaru 20 tana mulki, ba za ta iya warware dukkan matsalolin da ke fuskantar birnin ba, sai dai tana kokarin inganta rayuwar mazauna yankin.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 04 ga Agusta, yayin wata ganawa da ‘yan jarida a Abuja, inda ya mayar da martani kan batutuwan da suka shafi kaddamar da ayyuka da kuma irin ci gaban da ake samu a FCT.
“Ba zan ce an warware dukkan matsaloli ba. Babu wata gwamnati da za ta iya warware komai, ko da gwamnatin nan za ta yi shekaru 20 tana mulki. Amma gwamnati tana warware wasu matsaloli da za su taimaka wajen inganta rayuwar mutane,” in ji shi.
Da yake bayani kan dalilin da ya sa ba a kaddamar da wasu ayyuka da gwamnati ke yi ba, Wike ya ce gwamnati na bai wa manyan ayyuka da suka lakume kudade masu yawa fifiko, domin nuna tasirinsu.
“Muna daukar manyan ayyuka ne, wadanda aka kashe biliyoyin naira a kansu, domin nuna su. Amma idan ayyuka kanana ne, dole ne sai an kaddamar da su?”
Ya bukaci ‘yan jarida da su hada kai da gwamnati ta hanyar ziyartar wuraren da ake gudanar da ayyuka tare da sakatarorin da ke da hurumin lura da fannonin daban-daban kamar ilimi da walwala.
“Ba mu ce mun gama komai ba. Amma muna yin abubuwan da za su sauya rayuwar al’umma, kuma wannan shi ne ainihin manufar mulki,” in ji Wike.