Fashion
Gwamnatin Kano Ta Gudanar Da Bikin Ranar Al’adu Ta Duniya Karo Na Farko a Tarihi

Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da bikin Ranar Al’adu ta Duniya karo na farko a tarihin jihar – bikin wanda aka shirya domin tabbatar da matsayin Kano a matsayin cibiyar kasuwanci, ilimin addinin Musulunci, da kuma fasaha ta gargajiya.
Da yake kaddamar da bikin a zauren Coronation Hall, Fadar Gwamnati ta Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan biki ba wai kawai yana tunawa da kyakkyawan tarihinta ba ne, har ma wata dabara ce ta kara bunkasa fannin al’adu da yawon bude ido domin su zama ginshikan cigaban tattalin arziki da alfahari.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano a ranar Lahadi 03 ga Agusta, 2025.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da bangaren al’adu da yawon bude ido domin kare da yada al’adun Kano da suka shahara a duniya.
Ya ce: “Muna sake tsara dabarun zuba jari a fannin yawon bude ido domin jan hankalin masu ruwa da tsaki daga cikin gida da wajen kasa.”
Ya kara da cewa gwamnati na gudanar da shirye-shirye don horar da matasa da basu damar samun sana’o’i a bangaren yawon bude ido, ciki har da fasahar gargajiya, yawon bude ido, da bunkasa abincin gargajiya.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an kulla huldar hadin gwiwa da masu zuba jari na cikin gida da kungiyoyin al’adu na kasa da kasa domin shirya bukukuwa, musayar al’adu da kuma yada tarihin Kano a matakin duniya.
A nata jawabin, Kwamishinar Al’adu da Yawon Bude Ido, Hajiya Aisha Lawan Saji, ta yaba da goyon bayan Gwamna Yusuf wajen farfado da wannan fanni, tana mai jaddada muhimmancin sa wajen habaka tattalin arziki da kare al’adunmu.