Connect with us

Fashion

Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Kurkukun Kurmawa Zuwa Gidan Tarihi Da Al’adun Gargajiya

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin ta na mayar da kurkukun Kurmawa, wanda aka gina sama da shekara 115 da suka wuce, zuwa gidan tarihin al’adu domin ajiye tarihi da al’adun gargajiya na jihar.

An gina kurkukun Kurmawa a shekarar 1910 a cikin fadar Mai Martaba Sarkin Kano, karkashin mulkin mallaka na Birtaniya. An tsara shi domin ɗaukar fursunoni har guda 690.

Tsawon shekaru, Kurmawa ya kasance daya daga cikin manyan alamu na ikon turawan mulkin mallaka da tsarin gyaran hali a Arewacin Najeriya.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ya wallafa a dandalin Facebook da yammacin Lahadi 03 ga Agusta, ya bayyana cewa za a mayar da dukkan fursunonin da ke kurkukun Kurmawa zuwa sabuwar cibiyar gyaran hali da ke Janguza, kusa da barikin soja a kan hanyar Kano–Gwarzo–Dayi.

Ya rubuta cewa: “Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta mayar da dukkan fursunonin da ke Kurkukun Kurmawa zuwa Janguza, yayin da za a mayar da Kurkukun Kurmawa gidauniyar tarihin al’adu domin adana kayan tarihi da kuma inganta al’adun gargajiya na jihar.”

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet